An bayyana cewa, 'yan bindiga ne suka kashe wasu 'yan jaridar kasar Spaniya 2 da dan kasar Ailan 1 da suka bata a Burkina Faso.
A ranar 26 ga Afrilu ne a yayin da wasu mutane 40 'yan kasar Spaniya su ke yawon bude ido a filin shakatawa na Pama da ke gabashin Burkina Faso, aka nemi 'yan jaridar da wani jami'in tsaro 1 sama ko kasa aka rasa.
Bayan taron Majalisar Zartarwa ta Spaniya, Ministan Harkokin Wajen Kasar Gonzalez Laya ya sanar da duniya cewa, an gano gawarwakin mutanen 4, kuma an tabbatar da gawarwakin 2 daga cikinsu na 'yan jaridar Spaniya ne.
An bayyana cewa, 'yan jaridar sun hada da David Beriain da mai daukar hoto Roberto Fraile da suke daukar labaran gaskiya game da yankunan da aka haramta farauta.
Laya ya ce, "Wannan waje mai hatsari sosai, waje ne da 'yan ta'adda, masu farauta ba bisa ka'İda ba da kungiyoyin bata-gari suke zama a cikin sa."
An bayyana cewa, tare da 'yan jaridar 2 na Spaniya, akwai dan jaridar kasar Ailan da ma'aikacin tsaro dan kasar ta Burkina Faso.