Sojojin Majalisar Dinkin Duniya 3 sun mutu, wasu 6 sun jikkata sakamakon harin ta'ddanci da aka kai a yankin Tumbuktu na Mali.
Ofishin Dakarun MDD da Mali MINUSMA a sanar da cewa, sojojinsu sun gamu da harin ta'addanci a yankin Duentza na Timbuktu.
An bayyana mutuwar sojojin MDD 3 da jikkatar wasu 6 sakamakon harin na ta'addanci.
Shugaban MINUSMA Mahamat Saleh Annadif ya soki harin jan dakarunsu.
Tun shekarar 2013 zuwa yau dakarun MINUSMA su ke Mali kuma sun rasa sojojinsu 230.