Sojojin Faransa 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai musu a Mali.
Fadar Shugaban kasar Faransa Elysee ta fitar da rubutacciyar sanarwa inda ta bayyana cewar, an kai kai harin da bam wanda aka samar da hannu, kan mota mai sulke da sojojinta su ke ciki yayin kai farmakai a yankin Hombori na Mali.
Sanarwar ta ce, sojoji 3 sun mutu sakamakon fashewar bam din, kuma Shugaba Macron na jin irin radadin da sojojin ke ji, kuma yana mika sakon ta'aziyya gare su.
Sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Faransa ta fitar ta ce, an kai harin da safiyar Litinin din nan.
A karkashin farmakan Berkhane da Faransa ta fara kaddamarwa a shekarar 2014 a Murtaniya, Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, ta aika da sojoji dubu 5,100 zuwa kasashen.