Sojoji 7 sun rasa rayukansu sakamakon harin kwantar baunar da 'yan tawayen ADF suka kai a filin shakatawa na Virunga da ke arewa maso-gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce maharan da ake kyautata zaton na ADF ne sun shammaci dakarun soji a filin shakatawar tare da kai musu harin kwantan bauna.
Sojoji 7 ne suka mutu sakamakon harin.
A iyakokin gabashin kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Uganda, Burundi da Ruwanda tsawon shekaru 20 ana samun arangama sakamakon takaddamar wa ke da mallakin albarkatun zinariya da jan karfe da ke yankin.
Daga shekarar 2014 zuwa yau ADF ta kashe fararen hula dubu 3 a hare-haren da ta kai a yankin.