An kashe sojoji 5 a harin bam a Somaliya

An kashe sojoji 5 a harin bam a Somaliya

Sojoji 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Somaliya.

Wani jami'in 'yan sandan yankin Juba Abdurrahman Adan ya shaida cewa, an kai harin da safiyar Litinin din nan a filin tashi da saukar jiragen sama na Afmadov da ke kudancin kasar inda aka nufi jami'an tsaro.

Sojoji 5 ne suka mutu sakamakon harin na bam.

Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Al-Shabab na kai hari kan sojojin kasar, na Majalisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Afirka.


News Source:   ()