Sojoji 4 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar da suka yi da 'yan tawayen "Mai Mai Kata Katanga" a garin Lubumbashi na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Mambobin "Mai Mai Kata Katanga" sun kai hari kan ma'ajiyar makaman dakarun gwamnati da ke a waje mai nisan kilomita 10 daga tsakiyar garin Lubumbashi.
An kashe 'yan tawaye 12 tare da jikkata 4.
'Yan tawayen sun harba manyan makamai da suka hada da na roka kan ma'ajiyar makaman inda suka kashe sojoji 4.
'Yan tawayen "Mai Mai Kata Katanga" da ke karkashin jagorancin Gedeon Kyungu Mutanga na yaki don 'yantar da jihar Katanga mafi yawan arzikin arziki a kasar.