An kashe sojoji 3 a harin bam a Somaliya

An kashe sojoji 3 a harin bam a Somaliya

Sojoji 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai sansaninsu da ke kudancin Somaliya.

Kakakin gwamnati Isma'il Mukhtar Umar ya shaida cewar 'yan ta'addar Al-Shabab ne suka kai harin da mota dauke da bama-bamai kan sansanin soji na yankin Bay.

Umar ya ce an samu arangama tsakanin sojoji da 'yan ta'addar bayan fashewar, inda aka kuma kore su daga yankin.

Daya daga cikin jami'an soji na yankin Bay, Adan Kheyrow ya bayyana cewar an kashe sojoji 3 a harin.

Ya kuma ce an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab da yawa a arangamar da ta biyo baya.


News Source:   ()