An kashe sojoji 16 a Jamhuriyar Nijar

An kashe sojoji 16 a Jamhuriyar Nijar

Sojoji 16 da fararen hul 4 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a Jamhuriyar Nijar.

Sanarwar da aka fitar daga Rundunar Sojin Nijar ta ce, 'yan bindiga kusan 200 ne suka kai hari a yankin Banibangu na yammacin kasar, inda sakamakon mayar da martanin jami'an tsaro arangama ta barke.

Sanarwar ta ce, sojoji 16 da fararen hula 4 sun mutu, wasu sojojin kuma sun bata.

A 'yan kwanakin nan rikici na karuwa a yammacin Nijar.

Kasashen Sahel 3 da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso na fuskantar hare-hare daga 'yan ta'addar Daesh da ke da alaka da Alqa'eda.

 


News Source:   ()