A jihar Katsina dake Najeriya an yi nasarar bindige wanda ya jagoranci sace daruruwan dalibai maza daga wata makaranta har lahira.
A gandun dajin Dumburun dake tsakanin jihar Katsina da Zamfara ne rikici ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan fashin dajin biyu.
A rikicin an bindige shugaban 'yan fashin dajin Auwal Daudawa da ya jagoranci sace daruruwan dalibai maza a makarnatar sakadaren dake garin Kankara a ranar 11 ga watan Disamba.
'Yan fashin dajin dai sun kai hari a makarantar kwanan ta maza inda suka sace dalibai fiye da 500.
A yayinda aka kubutar da dalibai 287, a sulhun da aka yi da jami'an gwamnati a ranar 18 ga watan Disamba ne aka sako sauran daliban.
Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sanar da rufe dukkanin makarantar kwana dake fadin jahan.