Mutane 20 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka fafata da 'yan bindiga da 'yan kato da gora a jihar Niger da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Dan majalisar dokokin jihar Niger mai wakiltar mazabar Mariga Ibrahim Salisu ya ce, a kauyen Kotonkoro na yankin Mariga ne aka samu rikici tsakanin 'yan bindiga da 'yan kato da gora.
Iliyasu ya shaida cewa, bayan an aika da jami'an tsaro zuwa yankin ne aka gano jikkunan 'yan kato da gora 20 da aka kashe a rikicin.
Ya ce, sojoji sun karbe iko da yankin.