Mutane 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci na bam da aka kai da mota da kuma arangamar da aka yi a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Labaran da jaridun Somaliya suka fitar sun ce an kai harin kunar bakin wake da mota dauke da bama-bamai a kan wani gidan otel da ke Mogadishu.
Rahotannin farko da aka fitar sun ce mutane 17 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon harin.
Jami'an tsaro da aka kai yankin sun kubutar da mutane kusan 200.
Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.
Kungiyar Al-Shabab da ta kwace kauyuka da garuruwa da dama a Somaliya, na yawan kai wa jami'an tsaro da fararen hula hari a kasar.