Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a jihar Anambra da ke kudu maso-gabashin Najeriya.
Kakakin 'yan sandan Anambra Tochukwu Ikenga ya bayyana cewa, an aika da jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.
Ikenga ya kara a cewa, an shawo kan al'amura a yankin.
Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun ce, mutane 19 aka kashe sakamakon harin.
A gefe guda, an aiyana dokar hana fita waje a yankin sakamakon lamarin.