Mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a arewacin Burkina Faso.
An kai harin kan wata mahakar ma'adanan zinare da ke garin Arbind na yankin Soum.
An kashe mutane 8 tare da jikkata wasu da dama sakamakon harin.
Maharan sun kuma saci dukiyoyi da dabbobin jama'ar yankin.
'Yan ta'adda na yawan kai hare-hare a yankin Sahel da ya hada gabashi da arewacin Burkina Faso kuma iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Daga shekarar 2015 zuwa yau an kashe mutane sama da 900 tare da raba sama da miliyan guda da matsugunansu sakamakon hare-haren na ta'addanci a kasar.