An kashe mutane 50 a harin ta'addanci a Burkina Faso

An kashe mutane 50 a harin ta'addanci a Burkina Faso

Mutane 50 sun rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci da aka kai a Burkina Faso.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Petabouilli mai nisan kilomita 50 daga garin Gorom-Gorom.

'Yan ta'addar sun bude wuta kan fararen hula a kauyen inda mutane 50 suka mutu.

Tun shekarar 2018 ake samun kai hare-hare a yankunan arewacin Burkina Faso da suka hada da yankin Banh mai iyaka da kasar Mali.

Tun shekarar 2019 zuwa yau dokar ta baci ta ke ci gaba da aiyukan a yankuna 7 daga cikin 13 na Burkina Faso.

Kusan mutane miliyan 1 sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ta'addanci da ake kai wa a Burkna Faso tun shekarar 2015.


News Source:   www.trt.net.tr