Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka yi yayin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na 'Yan Majalisun Dokokin Gana.
Sanarwar da Rundunar 'Yan sandan Gana ta fitar ta ce, an samu rikici a yankuna 21 da aka gudanar da zabe a kasar.
An bayyana mutuwar mutane 5 tare a jikkatar wasu da dama sakamakon rikicin da aka yi.
Daraktan Aiyukan 'Yan sanda da Kare Jama'a ya shaida cewar, an dauki matakan hana rikici afkuwa, ya kuma soki tayar da zaune tsaye da wasu suka so yi.
A ranar 7 ga Disamba ne aka gudanar da zaben Shugaban Kasar Gana, inda Shugaba Mai Ci Nana Akupo-Addo ya samu kaso 51,59 na kuri'un da aka jefa wanda hakan ya ba shi damar sake yin wa'adi na 2.