A kalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addanci da aka kai a kauyuka 4 a lokaci guda a Mali.
Mataimakin gwamnan Ansongo, Oumar Kida ya shaida cewa, 'yan ta'addar sun kai hari kan kauyuka 4 da ke gundumar Ouatagouna da ke yankin Ansongo.
Mataimakin Shugaban Gundumar Ouatagouna Mahamane Bacala ya shaida cewa, 'yan ta'addar sun kashe mutane 17 a kauyen Karou, 7 a kauyen Dirgua, 14 a kauyen Deouteguef da 10 a Ouaragouna.
Mahukuntan sun bayyana jikkatar wasu mutanen da dama.
Ana fargabar adadin wadnd za su mutu zai iya daduwa.