Mutane 35 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a kudancin Chadi.
Jami'in yankin Salama, Mara Maad ya shaida cewa, sakamakon rikicin da aka yi kan filayen kiwon dabbobi, mutane 35 da suka hada da soja 1 sun mutu.
Maad ya ce, an fara rikicin tun ranar 15 ga Fabrairu, kuma tuni aka aike da jami'an tsaro zuwa yankin.
A watan Nuwamban bara an kashe mutane 22 a rikici makamancin wannan da aka yi a yankin.
Tsawon shekaru ana samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a kudancin Chadi bisa zargin dabbobi na cinye amfanin gonar manoma.