Mutane 33 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Shugaban Kungiyar hadin kan Al'ummar Kudancin Kaduna Luka Binniyat ya shaida cewar a ranar Alhamis din nan 'yan bindiga sun kai hare-hare a kauyukan Kurmin Masara, Apyia Shyim da Takmawai tare da bude wuta kan jama'a.
Binniyat ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren ya kai mutane 33, an kuma jikkata wasu da dama.
Shugaban Rundunar 'Yan sandan najeriya Muhammed A Adamu ya ce an tura karin jami'an tsaro da dama zuwa yankin.
An aiyana dokar hana fita waje a jihar Kaduna ta awanni 24 sakamakon hare-haren.