Mutane 3 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu 79 suka samu raunuka sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kabilun Bani Amir da Nuba da ke gabashin Sudan.
Gwamnan Kesele Mahmud Babekr ya fitar da sanarwar cewa a ranar Alhamis din makon da ya gabata husuma ta barke tsakanin kabilun Banu Amir da Nuba datsawon shekaru suke rikici da juna, jami'an tsaro sun kwantar da tarzomar amma washe gari ta ci gaba.
Gwamna Babekr ya ce an kashe mutane 3 tare da jikkata wasu 79 daga kablar Banu Amir inda aka kuma kona gidajensu da dama, sannan an kama mutane 59 daga kowanne bangare.
Tsawon shekaru ana samun rikici tsakanin kabilar banu Amir Larabawa kuma Musulmai da ke garin Port Sudan na gabar tekun Maliya da kuma 'yan kabilar Nuba da suke Kiristoci da masu bautawa dabbobi ba kuma ba Larabawa ba.