Mutane 3 daga iyali daya sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai ta sama a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Gidan rediyon yanar gizo na Garowe ya sanar da cewa, mutane 3 daga iyali daya sun mutu sakamakon harin bam ta sama da aka kai a Babban Birnin.
Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin da aka nufi Fadar Shugaban Kasar Somaliya.