An kashe mutane 25 a rikicin kabilanci a Najeriya

An kashe mutane 25 a rikicin kabilanci a Najeriya

Mutane 25 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin kabilanci da ya afku a jihar Ebonyi da ke kudu maso-gabashin Najeriya.

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya shaida cewa, an samu mummunan rikici a yankin Ohaukwu na jihar tsakanin kabilun Effium da Ezza.

Umahi ya sanar da mutuwar mutane 25 tare da jikkata wasu da dama a rikicin.

Umahi ya kara da cewa, an kona gidaje 125 da wasu gidajen sayar da man fetur, kuma mazaunan yankin sun bar matsugunansu saboda tsoro.

Ana yawan samun rikici a tsakanin kabilun da ke jihar Ebonyi sakamakon takaddama kan rabon albarkatun kasa da suke da su a yankunansu.


News Source:   ()