An kashe mutane 240 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

An kashe mutane 240 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

A watan Afrilun da ya gabata an kashe mutane 240 sakamakon arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Ofishin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya fitar da rahoto kan take hakkokin dan adam da aka yi a watan Afrilu a kasar.

A rahoton an fadi cewar a watan Afrilun da ya gataba 'yan bindiga da jami'an tsaro sun kashe mutane 240.

Rahoton ya ce wannan adadi ya karu da kaso 13 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Afrilun 2019, kuma jami'an tsaron kasar ne suka kashe kaso 49 inda 'yan bindiga suka kashe kaso 51 na mutanen su 240.

Rahoton ya kara da cewar an kashe mutanen a yankunan da aka dauki tsawon lokaci ana rikici a cikinsu.

Daga cikin wadanda aka kashe har da mata 34 da yara kanana 28


News Source:   www.trt.net.tr