Mutane 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a yankin arewa maso-yammacin Najeriya.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya shaida cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a yankin Faskari da ke jihar.
Isa ya ce an kashe mutane 18 tare da jikkata wasu da dama sakamakon harin.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa an kona gidaje da dama, kuma maharan sun kwashe kayan abincin jama'a.
Ya ce an aike da jami'an tsaro zuwa yankin, kuma tuni aka fara gudanar da bincike.
Kwanaki 4 da suka gabata an kai hari a jihar ta Katsina tare da kashe mutane 13.