An kashe mutane 17 a harin da aka kai a jihar Niger da ke Najeriya

An kashe mutane 17 a harin da aka kai a jihar Niger da ke Najeriya

Labaran da jaridun kasar suk fitar na sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga a kan babura ne suka kai hari a yankin Rijau na jihar Niger.

An kashe mutane 17 a harin, an jikkata wasu da dama.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Niger ya gasgata kai harin amma bai ce komai game da adadin wadanda aka kashe ba.

Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya fitar da rubutacciyar sanarwa inda ya bayyana an aike da jami'an tsaro zuwa yankin, ya kuma bukaci jama'a da su nutsu.

A wani labarin da jaridun Najeriya suka fitar an bayyana cewar wasu 'yan bindigar sun je yankin Shiroro na jihar ta Niger tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.

'Yan bindigar sun yi garkuwa da akalla mutanen kauye 10


News Source:   ()