An kashe mutane 15 sakamakon harin 'yan bindiga a arewacin Najeriya

An kashe mutane 15 sakamakon harin 'yan bindiga a arewacin Najeriya

Mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Kakakin 'yan sandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya shaida cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka hari a kauyen Gonar Rogo da ke jihar.

Jalige ya kara da cewar an kashe mutane 15 tare da jikkata wasu 5 sakamakon harin.

Ya fadi cewar maharan sun kona gidaje da kayan abinci da dama a kauyen, kuma mazauna kauyen da dama sun tsere saboda firgita da suka yi.

Jalige ya ce an aike da jami'an tsaro zuwa kauyen kuma tuni aka fara gudanar da bincike.


News Source:   www.trt.net.tr