Mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai kan wata motar bas a Somaliya.
Kakakin gwamnatin kasar Mohamed Ibrahim Moalimu ya shaida cewa, bam da ya fashe a lokacin da wata mota dauke da fararen hula ta ke wucewa ta kusa da shi a yankin Middle Shabelle ya yi ajalin mutane 15.
Motar ta tashi da safiyar Larabar nan daga Mogadishu zuwa Jowhar.
Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.