Mutane 118 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka gwabza tsakanin sojoji da fararen hula a Sudan ta Kudu.
Daraktar gudanarwa na jihar Tonj, Makuei Mabior ya sanar da cewar rikici tsakanin sojoji da fraren hula ya barke a ranar Asabar a lokacin da sojojin suka yi yunkurin cire mayafin da ke kan wani matashi wanda ya nuna kin amincewa da hakan.
Mabior ya kara da cewa an kashe sojoji 34 da fararen hula 84 tare da jikkata wasu da dama a musayar wutar da aka yi.
Mabior ya kara da cewar an lalata wuraren kula da lafiya da ke jihar wanda hakan ya sanya aka gaza kula da lafiyar wadanda suka jikkata.
Ana fargabar adadin wadanda za su mutu zai karu.
Ya ce fararen hula da yawa sun gudu dazuka don kubutar da rayukansu.
Kakakin Rundunar Sojin Sudan ta Kudu Lul Ruai Koan ya gasgata afkuwar rikicin inda ya ce an aika da jami'an tsaro zuwa yankin.