Mutane 11 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga da aka kai a jihohin Kaduna da Katsina da ke arewacin Najeriya.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a yankin Goska.
Aruwan ya ce, an kashe mutane 4 tare da jikkata wasu da dama a harin.
A harin da 'yan bindigar suka kai kauyen Zandam na Katsina kuma sun kashe mutane 7 da suka hada da dan sanda 1.