A Najeriya dake yammacin Afirka, an kashe mutane 108 a hare-haren 'yan bindiga a makon da ya gabata.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun bayyana cewa, 'yan ta'addar Boko Haram da 'yan bindiga sun kai hare-hare a yankunan kasar daban-daban tun daga ranar Litinin.
Sakamakon hare-haren mutane 108 sun mutu, wasu da dama kuma sun samu raunuka.
Bayan hare-haren, gwamnonin jihohi 17 na kudancin Najeriya sun gudanar da taro tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kira taron kasa tattaunawa.
Gwamnonin sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yiwa 'yan Najeriya bayani game da halin rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.