Mutane 10 sun rasa rayukansu, wasu 13 sun samu raunuka sakamakon harin bam da aka kai wa wata motar fasinjoji a Somaliya.
Jami'in 'yan sanda yankin Lower Shebelle Hussein Abdi Ali ya shaida cewar an kai wa motar bas karama dauke da fararen hula harin bam.
Ali ya ce an kashe mutane 10 yayin wasu 13 suka jikkata sakamakon harin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin amma kuma, 'yan ta'addar Al-Shabab na yawan kai hare-hare a yankin inda suke nufar jami'an tsaro da fararen hula.
Bayan kai harin dakarun sojin Somaliya sun kai farmaki a yankin na Lower Shebelle tare da kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 18.