Mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce 'yan bindigar sun bude wuta a yankunan Jama'a da Kaura na jihar Kaduna.
Mutane 10 sun mutu a harin yayinda wasu da dama suka samu raunuka, wasu daruruwa kuma sun bar matsugunansu.
A gefe guda, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita ta awanni 24 a jihar saboda ci gaba da samun hare-hare da ake yi.