Mutane 10 sun rasa rayukansu, wasu 47 kuma sun samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a wurare 3 daban-daban da kuma kai hari da bindigu a jihar Borno da ke arewa maso-gabashin Najeriya.
Labaran da jaridun Najeriya suka fitar na cewa, an samu fashewar abubuwa da kai hari da bindigu a yankunan Gwange, Kaleri da Bulabulin da ke Maiduguri Babban Birnin jihar Borno.
Mutane 10 sun mutu, wasu 47 kuma sun jikkata sakamakon fashewar da kuma harin.
Jami'an gwamnati sun bayyana cewa, an aike da jami'an tsaro zuwa yankunan kuma an fara gudanar da bincike.
Kungiyar ta'adda ta Boko Haram na yawan kai hare-hare a jihar.
A gefe guda, dakarun sojin Najeriya sun sanar da kwace yankin Marte na jihar Borno daga hannun 'yan ta'addar Boko Haram.
An kashe 'Yan ta'adda da dama, wasu kuma sun gudu sakamakon farmakin da aka kai musu a Marte.