Mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a jihar benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Wani jami'in yankin Agatu mai suna Usman Sulaiman ya bayyana cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan manoma da ke gonaki a wani kauye da ke yankin na Agatu.
Sulaiman ya ce an kashe mutane 10 a harin tare da jikkata wasu da dama.
Jami'in ya kuma ce an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti inda jami'an tsaro suka je yankin tare da fara gudanar da bincike.