Mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai a Nijar.
Maharan da ba a san ko su waye ba ne sun kai hari kan kauyuka biyu da ke yankin Tillaberi na Nijar.
Maharan sun kashe fararen hula 10 tare da cinnawa gidaje da yawa wuta.
Mahukuntan yankin sun ce, akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya dadu.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.