An samu barkewar rikici tsakanin dakarun kasar Yemen da mayakan kungiyar Houthi lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan fiye da mutane 60.
Dangane ga labaran da kafafen yada labaran cikin gidan kasar suka rawaito a garin Marib an yi dauki ba dadi tskanin dakarun Yemen da mamabobin kungiyar Houthi.
A rikicin da aka tafka a sassan garin daban-daban an kashe 'yan Houthi 34 inda kuma aka kashe daga cikin dakarun kasar Yemen 27.
Hukumar kasar ta bayyana cewa dakarun kasar sun yi nasarar dakatar da yunkurin mamayar da mayakan Houthi suka yi niyyar kaiwa yankunan garin Marib.