Fararen hula sama da 100 ake kyautata zaton sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai kan masu gudanar da bukin aure a yankin Mopti na Mali.
Ba a san waye ya kai harin ba a wani kauye da ake gudanar da bukin aure.
Gidan rediyon Studio Tamani da ke Mali ya bayyana cewar an kai harin ta sama a kauyen Bounti da ake gudanar da bukin aure a daren da yahade ranakun Lahadi da Litinin din da suka gabata.
Shugabar gungumar yankin Adama Griabata shaida cewar, ba a san waye ya kai harin ba, amma akwai yiwuwar mutane tsakanin 100 zuwa 150 sun mutu.
Shaidun gani da ido sun ce, an kai harin a lokacin da mutanen kauyen da dama su ke halartar bukuin auren, kuma da yawansu sun mutu.
Ba a kuma san adadin wadanda suka jikkata ba.