Fararen hula 58 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci da aka kai a Jamhuriyar Nijar.
An kai harin a iyakar Jamhuriyar Nijar da Mali.
Sanarwar da gwamnatin Nijar ta fitar ta ce, wasu mahara a kan babura ne suka kai hari kan 'yan kasuwa a kan hanyar dawowar su daga kasuwar dabbobi ta yankin Banibangou da ke Tillaberi.
Bayanan farko sun ce an kashe mutane 58 sakamakon harin.
Wasu majiyoyin sun yi ikirarin cewar an kashe mutane 65.
Har yanzu ba a san wa ya kai harin ba, amma ana zargin 'yan ta'addar Daesh da ke aiyukan a yankin tsawon wani lokaci suka kai.