An kashe fararen hula 32 a wasu kauyukan Mali 4

An kashe fararen hula 32 a wasu kauyukan Mali 4

Fararen hula 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da 'yan bindigar da ba a san ko su waye ba ne suka kai a wasu kauyukan Mali 4 da ke yankin Mopti.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce dandazon maharan sun kai harin ne a kauyukan jama'ar Dogon da ke gundumar Bankass.

Maharan dauke da makamai da suka fito daga bangaren iyakar Burkina Faso sun kai hare-haren a kauyukan Gouari, Djimdo, Panga Dougpou da Dialakanda tare da kashe fararen hula 32.

Majiyoyin yankin dan soji sun fadi cewar maharan sun yi babbar barna a kauyukan.

Sojojin Mali da ke da nisan kilomita 20 daga kauyukan, ba su iya zuwa wajen ba sai bayan maharan sun tafi.

Tun shekarar 2012 zuwa yau ake kai hare-haren ta'addanci da kuma samun rikici da aranama a tsakiya da arewacin Mali.

A shekarar da ta gabata an kashe mutane sama da 300 a rikicin da aka yi tsakanin kabilun Fulani da Dogon a Mali.


News Source:   www.trt.net.tr