A yankin Benghazi na Libiya, an kashe babban kwamandan mayakan Haftar Mahmud Al-Warfalli wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta ke nema saboda aikata laifukan yaki.
Labaran da jaridun Libiya suka fitar na cewa, an harbe Al-Warfalli da bindiga a kusa da jami'ar Likitanci da Larabawa da ke Benghazi.
An bayyana cewa, Al-Warfalli ya mutu sakamakon harin.
A shekarar 2017 ne Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta zargi Warfalli da aikata laifukan yaki bayan kashe mutane 33 a yankunan Benghazi daban-daban, sannan ya kuma sanya aka kashe wasu mutane 6 ba tare da yi musu shari'a ba.
A watan Satumban 2020 Tarayyar Turai ta sakawa Warfalli da wasu mutane 2 takunkumi sakamakon keta hakkokin dan adam a Libiya.
A baya, an ga yadda Warfalli da magoya bayansa suka din ga kashe fararen hula a Libiya.