An kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da dubu a Najeriya

An kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da dubu a Najeriya

A makonni 6 da suka gabata a yayin farmakan da aka kai a arewa maso-gabashin Najeriya an kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da dubu daya.

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanal Yusuf Tukur Buratai ya shaidawa 'yan jaridu cewar dakarunsa a yankin tafkin Chadi suna ci gaba da kai wa 'yan ta'addar Boko Haram hare-hare a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Buratai ya ce a makonni 6 da suka gabata an kashe 'yan ta'addar Boko Haram dubu 1,015 inda daruruwansu kuma suka gudu dauke da raunuka a jikinsu.

Buratai ya kara da cewar an kama wasu 'yan ta'addar 84 da ransu da lafiyarsu, kuma an kwace motocinsu 150 da manyan makamai da bama-bamai.

Ya ce an kuma kashe sojoji 11 a yayin kai farmakan.

A gefe guda kuma kakakin ma'aikatar tsaro ta Najeriya John Eneche ya fadi cewar a jihohin Katsina da Zamfara da aka kai an kashe 'yan bindiga sama da 200 da a 'yan shekarun nan suke tayar da zaune tsaye a jihohin.


News Source:   www.trt.net.tr