An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 27 a Somaliya

An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 27 a Somaliya

Sojojin Somaliya sun kai farmakai a yankin Lower Shebelle da ke kudancin kasar ina suka kashe 'yan ta'addarAl-Shabab 27.

Janaral daga Rundunar Sojin Somaliya, Abdihamid Muhammad Dirir ya bayyana cewar dakarunsu sun kai farmaki a unguwar Dug Garir da ke Lower Shabelle.

Dirir ya ce a yayin farmakan an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 27 da suka hada da manyan jami'ansu 2.

Janar Dirir ya kuma ce a shirye suke da su ci gaba da yaki da ta'addanci don ganin bayansa, kuma za su ci gaba da kai farmakai ba dare ba rana.


News Source:   www.trt.net.tr