An sanar da cerwa an yi nasarar kashe 'yan bindiga 135 a wani rikici na kwanaki uku da ya barke tsakanin makiyayay da manoma a arewa masu yammacin kasar Najeriya.
Dangane ga bayanan da suka fito daga mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Najeriya John Eneche an tabbatar da cewa an kai farmakai a ranakun Laraba da Alhamis a jahohin Zamfara da Katsina.
Eneche, ya tabbatar da cewa a farmakin an kassara 'yan bindiga 135 inda ya kara da cewa da yawan 'yan bindiga sun tsere da raunuka.
Jihar Zamfara dai ta kasance inda aka kwashe shekaru hudu ana tafka rikici tsaknain manoma da makiyaya da kuma wasu kabilu.
Fulani makiyaya na zargin cewa manoma na sace musu shanu a yayinda suke kiwo a yankunan tare da kuma kai musu hari.
A yankunan dai an yi ikirarin cewa kusan mutum dubu 2 suka rasa rayukansu inda wasu dubbai suka yi kaura daga gidajensu.