A farmakan da dakarun Najeriya suka kai a arewa maso-gabashin kasar, an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 48 tare da kubutar da mutane 11 da suka yi garkuwa da su.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Muhammad Yarima ya shaida cewa, sun kaiwa 'yan ta'addar Boko Haram farmaki a yankunan Chibok da Askira da ke jihar Borno.
Yarima ya shaida cewa, an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 48, wasun su da dama kuma sun gudu da raunukan da suka samu.
Haka zalika ya ce, an kubutar da mutane 11 da 'yan ta'addar suka yi garkuwa da su. An samu labarin 1 daga cikin wadanda aka kubutar na dauke da ciwo a jikinsa.