An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 41 a wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai a arewa maso-gabashin kasar.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Muhammed Yarima ya shaida cewa, an kaiwa 'yan ta'addar Boko Haram farmaki a yankunan Gulwa da Musuri Musuri da ke Gamboru Ngala a jihar Borno.
Yarima ya ce, an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 41, an kuma jikkata wasu da dama daga cikin su inda aka kuma kwace makamai da kayan yaki da yawa.
A farmakin da aka samu nasarar kubutar da mata da yara kanana 60 da 'yan ta'addar suka yi garkuwa da su, sojoji 4 sun mutu yayinda wasu da dama suka samu raunuka.