A Najeriya an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 27 a yayin farmakin da aka kai musu.
Mukaddashin Kakakin Ma'aikatar Tsaro ta Najeriya Bernerd Onyeuko ya shaida cewa, a farmakin da sojoji suka kai a jihar Borno an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 27, wasu da dama kuma sun gudu dauke da raunukan da suka samu.
Onyeuko ya kara da da cewa, an kubutar da mutane 29 da 'yan ta'addar suka yi garkuwa da su, an kuma kama mambobin Boko Haram 51.
A gefe guda kuma yara kanana 11 sun samu nasarar guduwa daga sansanin masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna.
Kwamishin Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa, sakamakon farmakan da ake kaiwa a jihar ya sanya 'Yan bindiga sauya matsugunansu.
Aruwan ya kara da cewa, a lokacin da 'yan ta'addar suke kokarin sauya matsuguni ne yara kanana 11 masu shekru 7 zuwa 11 suka samu nasarar guduwa.
Aruwan ya kuma ce, yaran na cikin koshin lafiya, kuma tuni aka mika su ga iyayensu.