An sanar da cewa jami'an sojin Najeriya sun gudanar da babban farmakin da suka yi nasarar kashe 'yan ta'adda ha guda 134.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar John Enenche ya shaidawa manema labarai cewa an gudanar da farmaki akan 'yan ta'addar Boko Haram da na ISWAP dake arewa maso gabashin Najeriya.
Enenche ya kara da cewa "A farmakin Kantana Jimlan da rundunar sojin ke ci gaba da gudanarwa ta na ci gaba da samun nasarori inda ta yi nasarar kashe mamabobin kungiyar 'yan ta'addar ISWAP 78 da kuma na Boko Haram 56"
Haka kuma ya nanata cewa kungiyoyin ta'addancin biyu dake aiki tare don tabarbare kasar Najeriya an kame mambobinsu har guda 16.
Enenche ya tabbatar da cewa farmakin da aka kaddamar a ranar 1 ga watan Mayu an yi nasarar kame makaman kungiyoyin da dama a yankin.