An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 10 sakamakon wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai musu.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Muhammad Yerima ya sanar da cewa, sojojin sun kawar da yunkurin 'yan ta'addar Boko Haram na kai hari a yankin Rann da ke jihar Borno.
A farmakin da aka kaiwa 'yan Boko Haram bayan sun kai harin an kashe mambobin kungiyar 10, wasu da dama kuma sun gudu dauke da raunukan da suka samu.
Yerima ya kara da cewa, an kwace bindigu da kyan fada da dama daga hannun 'yan ta'addar.