An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab sama da 100 a Somaliya

A makonni 3 da suka gabata an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab sama da 100 a farmakan da aka kai musu a Somaliya.

Tashar talabijin ta kasa ta Somaliya SNTV ta bayyana cewa, an shiga mako na 3 da fara kai farmakai kan 'yan ta'addar a yankin Middle Shabelle.

Ya zuwa yanzu an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab sama da 100.

Rundunar Sojin Somaliya a ranar 3 ga Yuni ta sanar da cewa, a yayin arangama da 'yan ta'adda a yankin Middle Shabelle Shugaban Runduna ta 6 Manjo Janar Mohamed Abdiwahid da ke da lakabin "Gorgor" wanda ya samu horo a Turkiyya ya mutu.


News Source:   ()