An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 50 a Somaliya

An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 50 a Somaliya

A kalla 'yan ta'adda Al-Shabab 50 aka kashe a wasu farmakai da aka kai musu a Somaliya.

Rundunar Sojin Somaliya ta shaida cewa, daga ranar 11 ga Yuni zuwa yau an kaddamar da farmakan kan 'yan ta'addar Al-Shabab a yankin Hiiraan.

An bayyana cewa, an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab a kalla 50 sakamakon farmakan da aka kai a yankin. An kuma lalata mafaka da maboyar 'yan ta'addar da dama.

'Yan ta'addar Al-Shabab na yawan kaiwa fararen hula da jami'an tsaro hare-hare a yankin.

A Somaliya da ake shirye-shiryen gudanar da zabukan da aka dage, sojoji na kaiwa 'yan ta'addar Al-Shabab farmakai.

Ya zuwa yanzu an kubutar da a kalla kauyuka 6 daga hannun 'yan ta'addar.


News Source:   ()