An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 25 sakamakon farmakin da aka kai musu a Somaliya.
Sanarwar da Ma'aikatar Yada Labarai ta Somaliya ta fitar ta ce, an kai wa Al-Shabab farmaki a yankin Galmudug da ke tsakiyar kasar.
An kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 21 a farmakin, an kuma kashe jami'an tsaron jihar 5.
Sanarwar ta kara da cewa, sakamakon farmakan da aka kaiwa Al-Shabab a Galmudug a watanni 2 da suka gabata an kwace yankuna masu muhimmanci daga hannunta.